Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Taron ya gudana ne a Otal ɗin Serena Quetta. Manyan masu jawabi, ciki har da Allama Sayyid Jawad Naqvi, tsohon Sanata Mushtaq Ahmad Khan, Maulana Anwar-ul-Haq Haqqani, Maulana Abdul Haq Hashmi, Maulana Dabir Hussain, Maulana Abdul Kabir Shakir, Barista Iftikhar Hussain, Maulana Sayyid Samiullah Agha, da kuma Babban Jami'in Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Muhammad Karimi Todeshki, sune sukai jawabi a wurin taron.
Sun bayyana cewa akwai takaici da ban tausayi a yau ga dukkan Al'ummar Musulmi - ciki har da masu mulkinta - sun yi shiru a gaban zaluncin Isra'ila. Wannan shirun yana daidai da tsayawa ga rashin adalci kuma abu ne da a gaban Allah ba a bun yarda ba.
Allama Sayyid Jawad Naqvi, shugaban ƙungiyar Tehreeke-Bidari Ummate-Mustafa, ya ce:
"Shirun Duniyar Musulunci Game Da Zalunci Shine Babban Goyon Baya Ga Isra'ila Kuma Shine Tushen Ƙarfafar Gwiwarta Wajen Ci Gaba Da Zubar Da Jininta".
Ya ƙara da cewa rashin kulawa ga mutanen Gaza da ake zalunta da kuma shiru kan laifukan da ake aikata akan bil'adama shine babban bala'i ga al'ummar Musulmi - a zahiri, yana daidai da mutuwarta.
Masu magana sun ce ana amfani da ƙasashe kamar Qatar, Masar, Saudiyya, Jordan, da Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin kayan aiki don kawo ƙarshen gwagwarmaya da Isra'ila. Ya jaddada cewa gwagwarmaya alama ce ta imani, yayin da abin da ake kira "zaman lafiya" a zahiri dabara ce ta yarda Isra'ila da kuma karɓar wulaƙanci.
Ya yi gargaɗin cewa Amurka da Isra'ila suna yin sabbin tsare-tsare, yayin da shugabannin Musulmi ke ɗaukar hanyar kunya a matsayin ceto. Sun ce shiru da sulhu su ne hanyoyin zuwa bauta wanda da yin suna ƙarfafa maƙiya ne kawai.
Your Comment